Ra′ayoyin ′yan Najeriya kan hirar Buhari da DW | NRS-Import | DW | 17.10.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

NRS-Import

Ra'ayoyin 'yan Najeriya kan hirar Buhari da DW

A Najeriya kungiyoyin rajin kare hakkin dan Adam da 'yan siyasa na mai da martani a kan hirar da shugaban kasar Muhammadu Buhari ya yi da tashar DW, inda ya tabo batutuwan da ke haifar da cece-kuce.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da mai masaukinsa shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da mai masaukinsa shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel

A hirar tasa da tashar ta DW, shugaban na Najeriya Muhammadu Buhari ya tabo batutuwa da dama, kama daga na yaukaka cinikayya a tsakanin kasashen biyu ya zuwa batun ci gaba da tattaunawa don sako sauran ‘yan matan Chibok bayan nasarar da aka samu ta sako 21 daga cikinsu. To sai dai batun martanin da ya sake mayarwa matarsa a kan kalaman da ta yi akan gwamnatinsa da ya kara jadadda matsayinsa a tambayar da aka yi mashi a hirara da DW, yafi daukar hankalin jama'a da ya sanya maida murtani. Ga kungiyoyin kare hakin dan Adam kamar na Mallam Awwal Musa Rafsanjani shugaban kungiyar kare hakin dan Adam ta CISLAC da ke Abuja, na ganin kalaman sun sabawa matsayin mata a kasar.

Kodayake ra'ayoyi sun sha bamban a kan wannan batu kamar yadda al'addu suka bambanta a kasar, amma ga Injiniya Buba Galadima jigo a jamiyyar ta APC ya ce akwai bukatar a yi hattara da al'amarin. A yayin da ake ci gaba da nazarin tasiri ko illar da kalaman ka iya yi ga yadda ake kalon Najeriya a matsayinta na jagora a Afirka ga Hon Ahmed Babba Kaita daya daga cikin masu nuna goyon baya ga kalaman shugaban Najeriyar, ya ce su a garesu lamarin ya yi dai-dai. Da alamun batun kalaman uwar gidan shugaban na Najeriya zai ci gaba da mamaye muhimman batutuwan da ya tattauna a kasar ta Jamus musamman batun cinikayya da taimakon juna a tsakanin kasashen biyu.

Sauti da bidiyo akan labarin