1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ra'ayoyin 'yan Najeriya a game da jam'iyyar APC

August 1, 2013

Bayan da hukumar zabe a Najeriya INEC ta sanar da yi wa sabuwar jam’yyar adawa ta APC rajista al'umma sun bayyana ra’ayoyinsu tare da bayyana kalubalen da ke gaban jam’iyyar.

https://p.dw.com/p/19IQL
Attahiru Jega, Independent National Electoral Commission Chairman, declares Nigeria's incumbent President Goodluck Jonathan as the winner of last Saturday's presidential election, in Abuja, Nigeria, Monday, April 18, 2011. Jonathan clinched the oil-rich country's presidential election Monday, as rioting by opposition protesters in the Muslim north highlighted the religious and ethnic differences still dividing Africa's most populous nation. (Foto:Sunday Alamba/AP/dapd)
Wahlen Nigeria Attahiru JegaHoto: AP

Tun lokacin da hukumar zabe zaman kanta Tarayyar Najeriya ta sanar da rajistar hadakar manyan jam'iyyun adawa a kasar zuwa jam'iyya daya mai suna APC babu wani abu da ake tattaunawa da ya wuce shigowar wannan sabuwar jam'iyya fagen siyasar Najeriya.

Kusan dukkan wurare na taruwar jama'a zancen dai guda daya ne ake muhawara a kan shi ne na samun nasarar fitowar wannan jam'iyya da ake ganin za ta kalubalanci jam'iyyar da ta shirya yin mulki na tsawon shekaru 50 ko ma fiye a kasar.

Wasu bangarorin al'ummar sun yi maraba da samun rajistar wannan jam'iyya saboda imani da suka yi cewa za'a samu sauyi a siyasar kasar.

Auf dem Bild: Parteizentrale PDP (Partei an der Macht in Nigeria) in Abuja, Nigeria. Foto: Ubale Musa, Haussa / DW
Shelkwatar PDP a AbujaHoto: DW/U.Haussa

Alh. Maikano Sanda wani mai goyon bayan sabuwar jam'iyyar adawa ta APC ne.

Zai yi wuya a iya karya lagon PDP

To amma wasu kuma na ganin babu abin da zai canza in aka yi la'akkari da irin karfi da jam'iyyar PDP mai mulki ta yi da kuma dadewa bisa karagar mulkin kasar.

Alh. Yusha'u Yakubu shi ne dan autan jam'iyyar PDP na ganin babu abin da zai sa cikinsu ya duri ruwa saboda rajistar wannan sabuwar jam'iyya.

Akwai kuma wadanda suka yi imanin cewa mawuyaci ne a samu sauyin da ake nema bisa la'akkari da yanayin siyasar kasar wanda suka ce na cike da son zuciya da kabilanci har ma da addinanci.

Talakawan kasar dai sun yi marhabin da samun nasarar wannan jam'iyya ta adawa saboda imani da suka yi cewa zata fitar musu kitse daga wuta kuma fitowarta alheri ne har ma ga jam'iyyar PDP.

Babban kalubale a gaban sabuwar jam'iyyar

Wasu bangaren kuma na ganin akwai gagarumin kalubale a gaban shugabannin sabuwar jam'iyyar musamman na yadda za ta raba mukamai tsakanin tsofin jam'iyyun da suka yi hadakar da kuma yadda za ta fitar da ‘yan takara da za su karbu.

Büro der Oppositionspartei "Actopm Congress of Nigeria" in Abuja, Address No. 16, Bissau Street, Wuse Zone 6, Abuja *** Bild von DW-Mitarbeiter Ubale Musa, 28. Januar 2013
ACN na cikin hadakar da ta kafa sabuwar jam'iyyar APCHoto: DW/U. Musa

Malam Abdulkadir Sale malami a sashin horar da ilimin kimiyyar siyasa na jami'ar jihar Gombe na ganin akwai kalubale gaban jam'iyyar musamman ma yadda za ta shiga sako da lungunar kasar don tallata kanta ga talakawan kasar.

Abu guda da yawancin ‘yan Najeriya suka amince da shi, shi ne fitowar wannan jam'iyya a irin wannan lokaci alheri ne ga demokradiyyar kasar musamman ganin jam'iyyar PDP mai mulki na tangal-tangal saboda rikicin da ya kakare mata a wuya.

Mawallafi: Aminu Suleiman Mohammed
Edita: Mohammad Nasiru Awal