1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron Rasha da Afirka cikin rikicin Ukraine

Abdourahamane Hassane
July 25, 2023

Nan gaba a tsakiyyar wannan mako a ranar Alhamis shugaban kasar Rasha Vladmir putin zai karbi Bakwancin takkwarorinsa na Afirka a taron Rasha da Afirka da za a yi a Saint Petersburg.

https://p.dw.com/p/4UMwY
Russland-Afrika-Gipfel in Sotschi 2019
Hoto: Valery Sharifulin/Tass/dpa/picture alliance

Ana sa ran shugabannin kasashen Afrika da dama za su halarci taron  ciki har da shugaban Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, a karo na biyu na wannan taro bayan na farko a da aka yi a shekarar  ta 2019 a Sochi, da ke gabar tekun Bahar al Aswad. Shugabannin za su tattauna batun watsi da Moscow ta yi da wata muhimmiyar yarjejeniya wadda tun daga bazarar shekarar  ta 2022 ta bai wa Ukraine damar fitar da kayayyaki zuwa kasashen duniya ciki har da Afrika