1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan bindiga sun saki basaraken Jos

December 31, 2021

Rahotanni daga Plateau Najeriya na nuna cewar yan bindiga sun saki babban basaraken gargajiya mai daraja ta daya Sum Pyem Chief Charles Mato bayan shafe kwanaki a hannunsu.

https://p.dw.com/p/4523W
Nigeria Boko Haram
Hoto: Lekan Oyekanmi/AP Photo/picture alliance

'Yan bindigar sun saki basaraken kauyen Gyanbos ne bayan wani artabu tsakaninsu da dakarun wanzar da zaman lafiya a jihar. Ismaila Yakubu Ajala dake zama sakataren kungiyar raya cigaba al'ummar Femawa a Najeriya ya ce har kawo yanzu babu labarin ko an biya kudin fansa ne kafin sako basaraken, kasancewar a baya wanda suka yi garkuwa da shi sun bukaci naira milyan 500.

A cikin sanarwar da babban kwamadan rundunar wanzar da zaman lafiyar ya fitar ta ce an kama kimanin mutane takwas dake da hannu a garkuwa da basaraken.