Paul Biya: Za mu murkushe masu neman ballewa | Labarai | DW | 01.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Paul Biya: Za mu murkushe masu neman ballewa

Gwamnatin kasar Kamaru, ta yi alkawarin shafe dukkanin masu fafutikar ballewa da ke yanki mai amfani da turancin Ingilishi, saboda abin da ya kira bazanar da suke wa tsaron kasar.

Shugaba Paul Biya na kasar Kamaru, ya yi alkawarin shafe dukkanin masu fafutikar neman ballewa daga kasar, wato mutanen nan da ke yanki mai amfani da Turancin Ingilishi, saboda abin da ya kira bazanar da suke wa tsaron kasar. A wani jawabin da ya yi da yammacin Alhamis, Shugaba Biya ya kuma ce mafusatan sun kashe akalla sojoji hudu tare da wasu jami'an 'yan sanda biyu cikin wannan mako.

Cikin watanni biyun da suka gabata ne dai aka rasa wasu fararen hula da dama a kasar ta Kamaru, lokacin da gwamnatin kasar ta kife masu da'awar ballewar, da suka ce ana nuna masu wariya. Bangaren na Ingilishin, na zargin mayar da su saniyar ware daga bangaren kasar mai amfani da Faransanci da kasar ta fifita.