1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Paris: Emmanuel Macron ya samu babban rinjaye a majalisa

Salissou Boukari
June 18, 2017

Sakamakon farko na zaben 'yan majalisar dokokin kasar Faransa ya tabbatar cewa jam'iyyar Shugaban kasar ta "Repulique en Marche da abokiyar kawancenta ta Modem sun samu babban rinjaye a majalisa.

https://p.dw.com/p/2etkE
Frankreich Präsident Macron
Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya na gaisuwa ga jama'aHoto: picture-alliance/abaca/L. Christian

Kimantawa ta farko da kafofin yada labarai suka yi kan sakamakon kaman yanda aka saba a zabukan kasar ta Faransa, na nuni da cewa bangaren na Shugaba Macron sun samu kujeru 395 zuwa 425 a majalisar dokoki. Jam'iyyar 'yan Republicains da abokiyar kawancenta ta UDI, ke a sahu na biyu da kujeru 97 zuwa 117, sannan jam'iyyar 'yan Gurguzu ta tsohon shugaban kasar na Faransa François Hollande ta zo ta uku da kujeru 29 zuwa 34, sai jam'iyyar La France Insoumise ta Jean Luc Melenchon da kujeru 12 zuwa 17, sannan ta biyar jam'iyyar Front National mai kyamar baki da kujeru hudu zuwa shida.(04 - 06).

Daga cikin manyan sauye-sauyen da shugaban kasar ta Faransa yake son aiwatarwa, sun hada da wasu jerin matakai da suka shafi ma'aikata, wanda gwamnatin da ta gabata ta François Hollande ta sha gagwarmayawa ta tsawon watanni shida tare da 'yan kwadagon da ke adawa da tsarin. Tuni dai gwamnatin ta Macron ta sanar da wasu jerin tattaunawa tare da kungiyoyin kwadagon kasar, inda ake ganin za a yi tattaunawa akalla 50 daga nan zuwa 21 ga wata mai kamawa na Yuli a wani mataki na neman samun fahimtar juna tsakanin bangarorin.