Paparoma ya yi kiran sulhu kan Koriya | Labarai | DW | 30.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Paparoma ya yi kiran sulhu kan Koriya

A wani mataki na sassauta zaman dar dar kan rikiicin Koriya ta Arewa da Amirka, shugaban darikar Katolika na duniya Paparoma Francis ya yi kiran sulhuntawa ta diflomasiyya.

Shugaban darukar Katolika na duniya Paparoma Francis ya yi kiran shiga tsakani domin sulhunta takaddamar da ke neman kunno kai tsakanin Amirka da Koriya ta Arewa.

Yace kasa kamar Norway na iya shiga tsakani domin sulhunta takaddamar wadda ke kara yin kamari da kuma ke da matukar hadari.

Paparoma Francis yace yaki ba alheri bane domin yana iya kaiwa ga salwantar rayukan bayin Allah wadanda basu ji ba basu gani ba.

Da yake jawabi ga 'yan jarida a cikin jirgin a kan hanyarsa ta komawa gida bayan ziyarar da ya kai Masar Paparoma Francis yace a shirye yake ya gana da shugaban Amirka Donald Trump akan batun. O-Ton....

Yace zan kira su, kasashen da ke cikin wannan rikici na Koriya ta Arewa. Zan kira su kamar yadda na kan kira shugabanni na wasu kasashe domin a tattauna a kuma sulhunta rikicin ta hanyar diflomasiyya.  Akwai masu shiga tsakani da dama a duniya da kan yi irin wannan aiki, kamar Norway misali.