1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaVatican

Paparoma ya jagoranci addu'o'in Easter a Vatikan

March 31, 2024

Shugaban darikar Katholika na duniya Paparoma Francis ya jagoranci gabatar da addu'o'i albarkacin Easter cikin daren da ya gabata a fadar Vatikan.

https://p.dw.com/p/4eHpI
Paparom Francis a lokacin addu'o'i na Easter a fadar Vatikan
Paparom Francis a lokacin addu'o'i na Easter a fadar VatikanHoto: Andrew Medichini/AP Photo/picture allliance

Paparoma Francis ya jagoranci addu'o'in na Easter ne kuwa kwana guda bayan janye jiki da ya yi a kusan karshen addu'o'in Good Friday da aka yi a ranar Juma'a saboda dalilai na kare lafiyarsa.

Kodayake a jiya Asabar ma ya gabatar da wa'azi na mintuna 10 kuma ya yi wa wasu mutum takwas wankan-tsarki na Baptisma.

Paparoma ya kuma yi kiran da a gaggauta tsagaita wuta a yakin Isra'ila da Hamas a Zirin Gaza da kuma musayar fursunoni a yakin da ake yi tsakanin Rasha da  kasar Ukraine.

Haka ma ya jaddada bukatar 

Cikin jawabin da ya gabatar a daren da ya gabata albarkacin bikin Easter da ake ciki, ya yi tir matuka a game da yake-yake da kuma kiyayya gami da kyamar juna a duniya.

Wasu dai na nuna damuwa game da yanayin lafiyar Paparoma Francis ganin yadda wasu daga cikin ayyukan ibadar lokacin na Easter suka wuce shi.

Fadar Vatikan ta ce yana fama ne da mura da kuma matsaloli da ke da nasaba da hanyoyin numfashi.