Panama Papers: Badakalar kaurace wa biyan haraji
April 7, 2016
Talla
Babbar kungiyar 'yan jaridu ta duniya masu bincike wato ICIJ ta wallafa sakamakon binciken da ta aiwatar, wanda kuma ya shafi manya-manyan mutane har da shugabannin kasashe akalla 12 inda shida daga cikinsu ke bisa mulki da kuma wadanda suka yi suna a fannin wasannin motsa jiki, da ke kaurace wa biyan haraji.