Panama Papers: Badakalar kin biyan haraji | Labarai | DW | 04.04.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Panama Papers: Badakalar kin biyan haraji

Wani bicike da gamayyar wasu jaridu fiye da 100 suka aiwatar bisa kudadan ajiya da kuma kaucewa haraji daga dukiyoyin manyan mutane a duniya na haifar da cecekuce.

A ranar Lahadi ce dai (03.04.2016) babbar kungiyar 'yan jaridu ta duniya masu bincike wato ICIJ ta fara wallafa sakamakon binciken da ta aiwatar, wanda kuma ya shafi manya-manyan mutane har da shugabannin kasashe a kalla 12 inda shida daga cikinsu ke bisa mulki da kuma wadanda suka yi suna a fannin wasannin motsa jiki.

Wannan bincike dai da aka wa suna "Panama Papers" an gudanar da shi ne tsawon shekara guda, kuma 'yan jaridu 378 ne suka aiwatar da shi a cikin kasashe 77 bisa wasu litattafai na boye da yawansu ya kai miliyan 11 da dubu 500 da suka fito daga wata cibiyar lauyoyi ta kasar Panama mai suna Mossack Fonseca wadda ta kware wajan kirkiro da kanfanoni.

Sai dai da yake magana kan wannan batu Ramon Fonseca daya daga cikin shugabannin wannan kanfani na lawyoyi da ke kasar Panama ye ce wannan kanfani na su ya shafe kusan sheru 40 yana aiki da kasuwannin duniya amma ba a taba samun shi da aikata wani abun da ba daidai ba.