Panama Papers wata badakala ce da aka bankado ta kafa masana'antun boge bisa tallafin lauyoyin cibiyar Mossack Fonseca domin kauce wa biyan haraji.
Wata kafa da ba ta so a bayyana sunanta ce ta baiwa jaridar "Süddeutsche Zeitung" ta Jamus bayanai kan tarin attajirai da ke kafa masana'antun boge a Panama. Su kuma 'yan jarida suka tona musu asiri.