Juan Damiani ya yi murabus daga hukumar FIFA | Labarai | DW | 06.04.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Juan Damiani ya yi murabus daga hukumar FIFA

Shugaban kwamitin da'a na hukumar kollon kafa ta duniya FIFA Juan Damiani ya yi muramus a wannan Laraba, bayan da aka ambato sunansa a badakalar Panama Pepers.

Juan Pedro Damiani

Juan Pedro Damiani

Kawo yanzu dai babu wani karin bayani da ya biyo bayan wannan murabus din daga hukumar kollon kafa ta duniya FIFA, wadda tun daga ranar Litinin ta soma bincike a kan wannan memba nata bayan da aka ambato sunansa cikin wannan badakala ta gujewa biyan kudadan haraji da wasu manyan masu arziki ke yi.

A cewar Masu binciken na Panama Pepers, an samu Juan Damiani da alaka da wasu mutane uku 'yan kasar Amirka da wata kotun ta Amirka ta gurfanar da su a badakalar cin hanci nan ta hukumar FIFA.