1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Pakistan ta saki matar da ta yi wa addini batanci

October 31, 2018

An tsaurara tsaro a Pakistan yayin da kotun kasar ke sakin matan da ta yi wa addinin Islama batanci a shekara ta 2010.

https://p.dw.com/p/37RKV
Pakistan Karachi Proteste nach Blasphemie Urteil
Hoto: Getty Images/AFP/A. Hassan

An dai baza jami'an tsaro a manyan biranen kasar, a kokarin dakile duk wani yunkurin kai hare-hare daga masu kaifin kishin addini, yayin da kotun ta sallami matar Kirista, Asia Bibi, wadda da ma aka yanke wa hukunci saboda batanci da ta yi wa addinin na Islama.

Bayanan da ke fitowa daga Islamabad babban birnin kasar, sun tabbatar da ganin wasu zaratan jami'an tsaron cikin shirin ko-ta-kwana, a wasu muhimman gine-ginen gwamnati, yayin da a share guda, masu kishin na addini suka ja damara.

Haka nan hukumomin birnin Lahore, sun gayyato sojoji bayan samun rahotannin kungiyar nan ta Tehreek-e-Labaik, na yunkurin kutsawa majalisar dokokin yankin.

A kudancin birnin Karachi ma, an ce wasu iyayen na gaggawar zuwa makarantu don kwaso 'ya'yansu saboda irin fargabar da ake ciki na yiwuwar tashin husuma.