1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Pakistan: PML-N da PPP za su kafa gwamnatin hadaka

February 21, 2024

Tsohon firaministan Pakistan Nawaz Sharif na shirin sake darewa kan madafun iko bayan cimma yarjejeniyar kafa gwamnatin kawance tsakanin manyan jam'iyyun siyasar kasar.

https://p.dw.com/p/4cdlJ
Pakistan | Bilawal Bhutto Zardari von der Pakistanischen Volkspartei (PPP) in Islamabad
Hoto: Aamir QURESHI/AFP

Duk da cewa dan takarar da jam'iyyar Imran Khan da ke garkame a gidan yari ta marawa shi ne ya samu rinjaye a zaben da aka gudanar a ranar takwas ga watan Fabarairu, to amma wannan kawance da aka kulla zai hana masa samun adadin 'yan majisar da yake bukata domin kafa gwamnati.

An dai share makonni ana tattaunawa kafin a amince a kulla kawancen wanda zai kafa gwamnatin hadaka da za ta tsayar da tsohon firaminista Nawaz Sharif wanda ya zo ta biyu a zaben a matsayin shugaban gwamnati sannan kuma Asif Ali Zardari mijin tsohuwar firaminista Benazir Bhutto da aka yi wa kisan gilla wanda ya zo na uku a matsayin shugaba.

Kazalika kawancen jam'iyyun biyu na PML-N da PPP ya kuma cimma yarjejeniyar raba wasu mukaman ministoci a tsanakinsu wadanda za a sanar cikin kwanaki masu zuwa.

To sai dai jam'iyyar Imran Khan da aka soke ta yi watsi da sakamakon zaben da ta ce an tafka magudi na mamaki tana mai ikirarin cewa dan takarar da ta marawa ya samun adadin kujerun da za su ba shi damar kafa gwamnati.