1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Pakistan: Kotu ta yankewa Imran Khan hukuncin dauri

January 30, 2024

Tsohon Firaiministan Pakistan kuma tsohon 'dan wasan kwallon cricket Imran Khan na fuskuntar shari'a daban-daban, tun bayan kuri'ar yankar kauna da ta kawo karshen gwamnatinsa a 2022.

https://p.dw.com/p/4bq7p
Tsohon Firaiministan Pakistan Imran Khan
Tsohon Firaiministan Pakistan Imran Khan Hoto: Akhtar Soomro/REUTERS

Kotun Pakistan ta yankewa tsohon Firaiministan kasar Imram Khan hukuncin daurin shekaru 10, sakamakon zargin fitar da wasu bayanan sirrin kasar, kamar yadda jam'iyyarsa ta PTI ta sanar.

Kazalika kotun ta kuma yankewa mataimakin shugaban jam'iyyar ta Pakistan Tehreek-e-Insaf PTI, wato Shah Mahmood Qureshi, shima daurin shekaru 10.

Hukuncin kotun na zuwa ne a daidai lokacin da ake shirye-shiryen gudanar da zabe a kasar ta Pakistan a ranar 8 ga watan Fabrairu 2024.

A martanin da ya mayar shugaban jam'iyyar ta PTI, Gohar Khan, ya ce za su kalubalanci hukuncin a kotun kolin kasar. Khan da Qureshi sun dai musanta zargin fallasa wasu daga cikin bayanan sirrin kasar tun a watan Oktobar da ta gabata.

A baya ma kotu ta yankewa Imran Khan, hukuncin daurin shekaru uku bayan samunsa da zargin cin hanci da rashawa, wanda daga bisani wata kotun ta wanke shi daga wancan zargi duk da cewa ana kuma tuhumarsa da aikata wasu laifukan na daban tun bayan kawar da gwamnatinsa a wata kuri'ar yankar kauna da al'ummar kasar suka yi a watan Afrilun shekara ta 2022.