1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karfafa dangantakar Iran da Pakistan

May 18, 2023

Kasashen Iran da Pakistan sun kaddamar da wata kasuwa a kan iyakar kasashen biyu, domin karfafa dangantakar da ke tsakaninsu.

https://p.dw.com/p/4RYAg
Pakistan | Iran | Dangantaka | Kan Iyaka | Kasuwanci
Firaminista Shahbaz Sharif na Pakistan da Shugaba Ebrahim Raisi na IranHoto: Pakistan Prime Minister Office/AP Photo/picture alliance

Rahotanni sun nunar da cewa Firaminista Shahbaz Sharif na Pakistan da Shugaba Ebrahim Raisi na Iran, sun kaddamar da kasuwar ne a kauyen Pashin da ke yankin Kudu maso Yammacin gundumar Baluchistan a Pakistan din. Wanna kasuwa dai na zaman guda cikin shida da kasashen biyu ke shirin kaddamarwa, a karkashin yarjejeniyar da suka kulla. Haka kuma Firaminista Sharif da Shugaba Raisi sun kuma kaddamar da tashar hasken wutar lantarki,  wadda za ta rin ka bai wa kauyukan karkarar Pakistan hasken wutar lantarkin daga Iran.