OPEC ta bayyana sabon shugabanta | Labarai | DW | 02.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

OPEC ta bayyana sabon shugabanta

An kammala taron kungiyar kasashe masu arzikin man fetur na OPEC a birnin Vienna ba tare da cimma wata matsaya ba, sai dai kungiyar ta bayyana sabon sakatare janar dinta.

Sabon sakatare janar na kungiyar OPEC Mohammed Sanusi Barkindo

Sabon sakatare janar na kungiyar OPEC Mohammed Sanusi Barkindo

Sakatare janar na kungiyar mai barin gado Abdallah Salem El-Badri ya bayyana cewa mambobin kungiyar dai na bukatar lokaci kafin su yanke hukunci na karshe dangane da batun da ya shafi farashin man da ma sayar da shi a kasuwannin duniya. Haka kuma kungiyar ta bayyana Mohammed Sanusi Barkindo a matsayin sabon sakatare janar na kungiyar, kamar yadda mai magana da yawun kungiyar Hasan Hafidh ke cewa:

"Taron ya amince da Mohammed Sanusi Barkindo daga Najeriya a matsayin Sakatare janar na kungiyar, wanda zai fara aiki daga ranar daya ga watan Augusta mai zuwa. Zai shafe tsahon shekaru uku yana jagorantar kungiyar. Haka kuma muna mika godiyarmu ga Abdallah Salem El-Badri bisa kakkyawan jagorancin da ya yi wa kungiyar."