Obama ya taya Buhari murnar lashe zabe | Labarai | DW | 01.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Obama ya taya Buhari murnar lashe zabe

Shugaban na Amurka ya yaba wa Muhammadu Buhari da shugaba mai barin gado Goodluck Jonathan dangane da nasarar gudanar da zabe cikin lumana.

Hakan na kunshe cikin sakon Obama zuwa ga al'ummar Najeriya, da acewarsa ko shakka babu na tabbatar da matsayin kasar na uwa mabada mama a nahiyar Afirka. Kan haka ne ya yi kira ga magoya bangarorin biyu da su ci-gaba da martaba demokradiyya ta hanyar darajawa sakamakon zaben, domin ci-gaban zamantakewa tsakanin al'umma da hadin kan kasa.

Shi ma a nashi sakon taya murna ga Buhari, babban sakataren MDD Ban Ki-moon, yabawa 'yan Najeriyar ya yi da cewar, sun taka rawar azo a gani. Ya ce gudanar da zaben cikin nasara na tabbatar da cewar yanzu Najeriya ta zama ja gaba a fannin demokradiyya. Ki-moon ya yi fatan cewar irin wannan halin sanin ya kamata ne zai kasance a zaben gwamnoni da na 'yan majalisar jiha da ke tafe a ranar 11 ga watan Afrilu. Acewarsa dai wannan yanayi abun yabawa ne, domin shi ne karon farko da wata gwamnatin farar hula za ta mika mulki zuwa ga wata, a wannan kasa da tafi ko wacce yawan jama'a a nahiyar Afrika.

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya shawarci 'yan takarar da ke da wani korafi da su gabatar da shi a hukumance.