Obama ya koka kan ayyukan ′yan ta′adda | Labarai | DW | 13.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Obama ya koka kan ayyukan 'yan ta'adda

Shugaban Amirka Barack Obama ya ce ba za a iya kawo karshen ayyukan 'yan ta'adda masu kaifin kishin addini da suka addabi duniya ta hanyar daukar tsauraran matakai na fushi a kansu ba.

Shugaba Barack Obama na Amirka

Shugaba Barack Obama na Amirka

Obama ya bayyana hakan ne yayin da ya ke jawabinsa na bakwai kuma na karshe a matsayin shugaban kasa a gaban majalisar dokokin kasar. Ya kara da cewa sun dauki yakin da suke da kungiyar 'yan ta'addan IS tamkar yakin duniya na uku, a yayin da mayakan ke hallaka rayukan al'umma wanda ya zamo wajibi a dakatar da ayyukansu.

Ya ce: "Mayaka masu yawa na makare bayan mayan motoci kirar pickup, kuma suna daukar rayukan mutane a gidaje da guraren taruwar jama'a, sun kasance babbar barazana ga rayuwar fararen hula. Tilas ne a dakatar da su."