Obama ya gana da Buhari a Washington | Labarai | DW | 20.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Obama ya gana da Buhari a Washington

Shugaban Amirka Obama ya yaba da matakan da shugaba Buhari na Najeriya ke dauka wajen yaki da kungiyar Boko Haram mai fada da makamai a arewacin kasar.

Shugaban kasar Amirka Barack Obama ya yaba da matakkan da shugaban kasar Najeriya Muhamadu Buhari yake dauka wajen yakar kungiyar Boko Haram mai yaki da makammai a kasar tun a shekara ta 2009. Obama ya yi wannan yabo ne ga shugaba Buhari lokacin ganawar da suka yi a fadar White House a mataki na farko na wata ziyarar aiki ta kwanaki da ya soma a kasar ta Amirka.

Shugaba Obama ya kuma ce a bayyane take cewar da gaske shugaba Buhari yake a shirinsa na yakar kungiyar ta Boko Haram dama duk wasu ayyukan ta'addanci da na cin hanci da karbar rashawa a Najeriya dama Afrika baki daya.Ya kuma kara da cewa za su tattauna da shugaba Buhari a kan yanda kasashen biyu za su yi aiki kafada da kafada wajen yakin da ayyukan ta'addanci dama cin hanci da rashawa a kasar ta Najeriya.