1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Obama ya caccaki Trump kan yaki da corona

Abdullahi Tanko Bala
May 10, 2020

Tsohon shugaban Amirka Barack Oabama ya yi kakkausar suka ga yadda shugaba Trump yake tafiyar da yaki da annobar corona.

https://p.dw.com/p/3bzbz
Kombobild Barack Obama - Donald Trump

Obama yace matakan da Trump ke dauka suna cike da tabargaza da rashin tsari. Ya yi wadannan kalaman ne a lokacin da yake tattaunawa da wasu tsoffin jami'an gwamnatinsa.

Mutane fiye da 77,000 suka rasu a Amirka a sakamakon annobar ta coronavirus yayin da adadin wadanda suka kamu da kwayar cutar a Amirka ya haura mutum miliyan daya da dubu dari uku.

A halin da ake ciki dai wasu jihohin Amirkar na shirin fara bude harkokin yau da kullum yayin da jami'an lafiya ke sa ido game da yiwuwar sake barkewar annobar a karo na biyu.

A waje guda kuma kasashen China da Koriya ta Kudu sun ruwaito karuwar sabbin kamun cutar ta Coronavirus a yau Lahadi, abin da ya tada hankali a kasashen da annobar ta yi sauki.

China ta baiyana sabbin kamu mutum goma sha hudu da suka harbu da cutar yayin da Koriya ta arewa ta ce ta sami mutane 34 da suka kamu da cutar a yau Lahadi.