1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tarihi

Oba Ewuare: Sarkin Tagulla na birnin Benin

Gwendolin Hilse MAB/MNA
September 24, 2020

Fiye da karni biyar bayan sarautarsa, gadon da Oba Ewuare ya bari na nan daram a cikin garin Benin. Ana tunawa da karfin ikonsa da kuma habaka fasahar sarrafa tagulla da ake cin amfani har yanzu.

https://p.dw.com/p/3itEX
African Roots | Oba Ewuare 1 | Porträt

Yaushe Oba Ewuare ya rayu?

Oba Ewuare, wanda kuma aka sani da Oba Ewuare I ko Ewuare Mai Girma, ya jagoranci tsohuwar masarautar Benin daga 1440 zuwa 1473. Ya zama Sarkin Benin bayan ya yi amfani da karfi wajen hambarar da dan uwansa daga gadon sarauta. Wannan Juyin mulkin ya jefa birnin Benin cikin komabaya, amma ya sami damar sake gina garin, har ma ya maida shi abin da daga baya ya zama daya daga cikin manyan daulolin da suka fi fice a Yammacin Afirka.

Yaya sarautar Oba Ewuare ta kasance?

A zamanin mulkin Ewuare, an tsara babban birnin masarautar Benin yadda ya kamata, kuma yana dauke da adadi mai yawa na al'umma. An ce ya gina wasu kofofi tara na shigowa Benin city kuma ya kula da ginin hanyoyi da yawa. Labarai na baka wadanda ba rubutattu ba, sun baiyana shi a matsayin babban matsafi, likita kuma jarumi.

Wace fasaha Oba Ewuare na Benin ya shahara a kai?

Bunkasar ayyukan fasaha a Benin ya kasance daya daga cikin muhimman gado da ake tuna Oba Ewuare da shi. Ya gayyaci masana fasahar zane-zane da kere-kere na garin da su dukufa wajen samar da fasaha mai inganci. Bugu da kari, ya bullo da kirar kawunan tagulla don girmama sarakunan Benin da suka mutu. Sun kasance kere-kere masu matukar muhimmanci a cikin gidajen adana kayan tarihi a Najeriya da kuma sassa na duniya. Habaka aikin fasaha da Ewuare ya yi ya haifar da kafa masana'antar sassaka hauren giwa da katako da tagulla wadanda har yanzu ake cin gajiyar su.

Oba Ewuare: Sarkin Tagulla na birnin Benin

Yaya aka bunkasa al'adu a karkashin mulkin Oba Ewuare?

Kazalika Oba Ewuare ya yi shuhura wajen inganta ayyukan al'adun Benin. Ya gabatar da bikin Igue wanda ya kasance daya daga cikin muhimman al'adun mutanen kasar Benin. Hakanan kuma, Oba Ewuare ya gabatar da murjani masu launin shudi a cikin Benin, wadanda a yau suka zama kayan ado na sarauta da kuma al'adun gargajiyar Benin. A yau, amfani da murjani bai tsaya a masarautar Benin kawai  ba. Amma ya bazu sosai zuwa sauran sassa na Kudancin Najeriya - godiya ta tabbata ga Oba Ewuare da ya samar da wannan tsarin kwalliya.

Mene ne sauran nasarorin Oba Ewuare?

Ewuare Babba ya kasance Oba na farko na Benin ba wai saboda shi ne farkon wanda ya fara mulkin masarautar Benin ba,  amma saboda shi ne Oba na farko da ya sauya masarautar. Ya gaji karamar masarauta amma ya fadadata sosai inda ya hada garuruwa da kauyuka da yawa. Matakan gudanarwa da ya fara dauka don tabbatar da mika mulki cikin lumana ya kasance abin da ake tunawa da shi har zuwa yau.  Kafa sharadin gadar mulkin da ya yi - ma'ana maye gurbi idan sarki ya  rasu babban dansa ya gaje shi, ya kawo karshen gwagwarmayar neman karbe iko tsakanin 'ya'yan sarki.

Shawarwarin gina wannan labarin sun samu ne daga masanan tarihi Farfesa Doulaye Konaté, Lily Mafela, Ph.D., da Farfesa Christopher Ogbogbo. Shirin African Roots ko Tushen Afirka na samun tallafi daga Gidauniyar Gerda Henkel.