1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martani kan yarjejeniyar Isra'ila da kasashen Larabawa

Mahamud Yaya Azare AMA
September 17, 2020

Kasashen Yankin Gabas Ta Tsakiya na ci gaba da martani kan kulla yarjejeniyar huldar jakadanci tsakanin Isra'ila da kasashen Bahrain da Hadaddiyar Daular Larabawa a Amirka.

https://p.dw.com/p/3icPq
USA Washington Weißes Haus | Abkommen Naher Osten
Hoto: Getty Images/AFP/S. Loeb

Al'ummar Falalsdinawa da ma na yankin Gabas Ta Tsakiya na ci gaba da mayar martani kan yarjejeniyar kasashen Hadaddiyar Daular Larabawa da Irsa'ila, kwana daya bayan da aka rattaba hannu kan yarjejeniyar mai dimbin tarihi a tsakanin asashen. Kasar Masar na a matsayin kasa ta farko da ta yyi marhabin lale da wannan yarjejeniyar, tare da mai bayyana fatan ganin cimma wannan matsayar ka iya taimawa wajen kafa kasar Faladinu a yankin. Shekaru 25 da suka gabata kasar Masar da Jodan sun kulla wannan hulda irin wannan da Isra'ila, sai dai hakan bai kai ga samar da zaman lafiyar da kasashen Larabawa ke fafutikar samu ba. Kungiyar kasashen yankin Larabawa ta nuna cewa a yanzu ba wasu muhimman wuraren da suka rage a yankin Falasdinu ba duba da yadda Isra'ila ta ci gaba da mamayesu, saboda haka idan dama ta kiya sai a koma hagu, ta hanyar sake wani sabon salo na neman gwada yarjejeniyar da ka iya kai kasar Falasdinawa ga kafuwa ta hanyar sake wani sabon salo na kusantar juna. Kasar Saudiyya ta bayyana matsayarta kan batun inda ta ce ba zata aminta da yarjejeniyar ba muddin ba a kai ga samun zarafin kasa kasar Falasdinawa ba, a yayin da ita kuwa kasar Iran da ta kira kasashen Bahrain da Hadaddiyar Daular Larabawa a matsayin barazana ta nuna cewa za ta ci gaba da fatali da huldarsu da Isra'ila, a yayin da ita kuwa hukumar Falalsdinawa ta sanar da yanke alaka da kasashen Bahrain da Hadaddiyar Daular Larabawa, tare da bayyana anniyarta na shirin ficewa daga cikin kungiyar Masu sharhi da dama cewa kulla hulda da Isra'ila da kasashen suka yi zai taimaka wajen dakile katsalandan din da kasar Iran ke yiwa kasashen yankin Gabas Ta Tsakiya, a yayin da wasu masanan ke fassara kulla yarjejeniyar a matsayin wata barazana ga yankin.