Nnmadi Kanu ya yi watsi da belin kotu. | Labarai | DW | 25.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Nnmadi Kanu ya yi watsi da belin kotu.

Nnamdi Kanu mai fafutukar rajin kafa kasar Biafrah yace ba zai iya cika sharuddan beli cikin sa'oi 24 da kotu ta bashi ba, saboda haka baya bukata.

Jagoran fafutukar kafa kasar Biafrah a Najeriya Nnamdi Kanu ya yi watsi da belin da wata kotun tarayya da ke Abuja ta bayar na sakinsa daga gidan wakafi bisa hujjar rashin koshin lafiya.

A ranar Talatar nan ce dai babbar kotun tarayyar ta Abuja karkashin jagorancin mai shari'a Binta Nyako ta bada umarnin belin bayan da ta baiyana cewa ta gamsu Kanu shugaban kungiyar IPOB mai rajin kafa kasar Biafrah ba shi da cikakkiyar lafiya a tsawon lokacin shari'ar da ake tuhumarsa akan su. A saboda haka ta ce ta bada belinsa bisa hujja ta rashin lafiya.

An ruwaito lauyan Kanu na cewa sharuddan da aka gindaya masa sun yi tsauri yadda ba zai iya cika su cikin sa'oi 48 ba.

Ita dai kotun ta umarci Kanu ya biya kudin ajiya na Naira miliyan 300 sannan ba zai halarci dukkan wani taron gangami ko shiga cikin wani ayari da ya wuce mutum goma ba, haka kuma ba zai yi hira da dukkan wata kafar yada labarai a tsawon wa'adin belin ba.