Nnamdi Kanu zai bayyana a gaban kotu | Labarai | DW | 08.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Nnamdi Kanu zai bayyana a gaban kotu

Babbar kotun tarayya a Najeriya ta amince da boye shaidu a shari'ar Nnamdi Kanu dan rajin samun 'yancin kan Biafra da zai bayyana a gaban kotun daga ranar Laraba.

Politischer Aktivist IPOB Nwannekaenyi Nnamdi Kenny Okwu Kanu im Gerichtssaal in Abuja

Nnamdi Kenny Okwu Kanu

Mai shari'a James Tsoho na babban kotun ya ce, ya aminta da daukar dukan matakan da suka dace na ganin cewar alkalai da sauran lauyoyi ne za su gana gaba da gaba da shaidun. Sai kuma shi wanda ake yi wa wannan shari'a Nnamdi Kanu da ke a matsayin darektan Radio Biafra sannan jagoran 'yan awaren. Tun farko dai wanda ake zargin ya musanta dukannin laifukan da ake zarginsa da su da suka hada da neman ayyana yaki ga Najeriya.

Shekaru bakwai ne dai bayan samun mulkin kai na Najeriya, wani rikici ya barke na neman raba kasar domin samun wata kasa mai suna Biafra a shekarun 1967 zuwa da 1970, yakin da ya haddasa rasuwar mutane a kalla miliyan daya.