Nkurunziza na son yin tazarce zuwa 2030 | Labarai | DW | 27.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Nkurunziza na son yin tazarce zuwa 2030

Majalisar ministocin gwamnatin Burundi ta amince da gyaran kundin tsarin mulki don bai wa shugaba Pierre Nkurunziza damar tazarce.

Majalisar gudanarwar gwamnatin Burundi ta amince da wani daftarin doka da zai yi kwaskwarima ga kundin tsarin mulkin kasar wanda kuma zai baiwa shugaba Pierre Nkurunziza damar ci gaba da mulki har zuwa shekara ta 2030.

Wani babban jami'in gwamnatin ya sanar da hakan.

Zanga zangar adawa da cigaba da mulkin Nkurunziza da 'yan kasar suka shafe shekaru biyu da rabi suna yi dai ya tilastawa mutane kimanin dubu 400 gudun hijira zuwa wasu kasashe.

Jami'in wanda ya bukaci a saya sunansa saboda bashi da izinin yin magana da kafofin yada labarai ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa an amince da kudirin dokar tun a ranar Talata.