1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nikolas Sarkozy ya sauka Tchad a kan rikicin "l Arche de Zoe"

November 4, 2007
https://p.dw.com/p/C14x

Kotun ƙasar Tchad, ta yi belin ´yan jarida 3 , da kuma yan mata na ƙasar Spain, da ke cikin tawagar „l´Arche de Zoe“, ƙungiyar nan da ake zargi da yunƙurin safara ƙananan yara.

A yau, shugaban ƙasar France Nikolas Sarkozy ya ziyarci ƙasar Tchad, a game da wannan batu.

Tun jiya Kotuna a Tchad, su ka fara sauraran 8, daga turawan 16, saidai baki ɗaya, sun mussanta zargin da ake masu.

A na kyauttata zaton, shugaba Sarkozy, zai ɗauko yan jarida 3,amma gwamnatin ƙasar Spain, ta mussanta batun cewar, shugaban, zai tafo da yan matan Spain, masu ɗawainiya a cikin jirgin, da aka tsara zai jigilar yaran.