Nijeriya: Muhawara kan matakin tsaron noma | Siyasa | DW | 21.07.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Nijeriya: Muhawara kan matakin tsaron noma

A Najeriya matakin da gwamnati ta dauka da ya tanadi cewar nan gaba manoma su za su dauki nauyin jami'an tsaron da za su kare su daga hare-hare ko yin garkuwa da su, ya soma haifar da muhawara a kasar.

Halin da yanayin tsaron ya shiga a Najeriya da a yanzu ya shafi aikin gona inda sannu a hankali hare-haren da ake kai wa da kuma ake dangata su da masu satar shanu da garkuwa da jama’a ya kara jefa tsoro ga manoma da dama, abinda ya sanya bukatar neman mafita.

Domin ta kai ga a wasu jihohin duk gonar da ta zarta kilomita biyar to sai dai manoma su sanya mata ido, domin in ba a yi kai wa masu aikin gona harin ba, to a yi garkuwa da su. Wannan ya sanya ministan kula da harkokin noma bayyana cewa za’a kyautata tsaro ga manoman amma fa manoman za su biya ta aljihun su. Shin masana harkokin tsaro mai za su ce kan wannan mataki? Malam Kabiru Adamu kwararre ne a harkar tsaro a Najeriya.

‘’Duk inda aka ce a sa kudi a harakar tsaro shi ke kawo cin hanci da rashawa, wanda matsalar da muke fama da ita kenan, kuma ma dai babban kuskure ne a ce za a dauki irin wannan mataki, domin ta kai ga fa a wasu wurare ba a iya zuwa gona. Ina talaka manomi ya ga kudin da zai biya don a kula da gonarsa’’

Gwamnatin Najeriyar dai na daukan wannan mataki ne a dai dai lokacin da take kara zaman shirinta na fadada hanyoyin samar da kudadden shigarta ta hanyar aikin gona a cikin kasar, a dai dai lokacin da al'ummar kasar ta kara rungumar harakar noman domin samun wadata kasa da abinci.

Nigeria - Landwirtschaft bei Katsina

Tuni dai hadaddiyar kungiyar manoma da masu sayar da amfanin gona ta Najeriya ta bakin shugabanta Malam Musa Labaran ta koka da wannan mataki na tsaro da kuma matsalar rashin isasshen taki da ta ce babbar barazana ce ga aikin noman daminar bana a kasar ta Najeriya

Kokarin shawo kan matsalar tsaro da ke shafar aikin noma a Najeriya dai babban kalubale ne da ke fuskantar gwamnatin kasar a yanzu, musamman sanin muhimmancin samar da abinci a kasa irin ta Najeriya da ke kokarin rage dogaro a kan shigo da abinci daga kasashen waje.

To sai dai ga Mallam Kabiru Adamu na ganin dole ne fa a sake lalle a kan wannan batu, domin daga kin gaskiya fa sai dai bata.

Abin jira a gani shi ne mataki na gaba da gwamnati za ta dauka a dai dai lokacin da take kwance kallabi sabon tsarin bunkasa aikin gona a kasar, wanda wajibi ne a nemo hanayr shawo kan batun tsaron domin samunn nasararsa.

Sauti da bidiyo akan labarin