1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Tsoffin sojoji da 'yan sanda za su koma aiki

Ramatu Garba Baba
December 14, 2022

Gwamnatin Nijar ta nemi taimakon jami'an 'yan sanda da sojoji da suka yi ritaya, da su dawo aiki don taimaka mata dakile 'yan ta'adda da suka hana zaman lafiya a kasar.

https://p.dw.com/p/4Kwkv
Hoto: AFP/S. Ag Anar

Gwamnatin jamhuriyyar Nijar ta bukaci tsoffin sojoji da jami'an 'yan sanda da suka riga suka yi ritaya da su dawo aiki don taimaka mata yakar mayakan jihadi da suka hana zaman lafiya a wasu sassan kasar.

A cewar Kanal Abdoulaye Mounkaila wani tsohon sojar kasar, ya ce, ana bukatar hadin kan tsoffin sojojin da suka riga suka yi wa kasar hidima, don hada karfi da karfe a murkushe aiyukan ta'addanci, ya kara da cewa, ba wai za a tura su fagen daga ba ne, amma za a tsugunar da su ne a yankunan da aka fi fuskantar barazanar tsaro. Tuni aka ware mako guda don gudanar da aikin rijistar tsoffin jami'an da suka amsa kiran gwamnatin.

Tun daga shekarar 2015 Nijar ta soma fuskantar tsananin matsalar tsaro daga masu ikirarin jihadi da suka kwararo cikin kasar daga kasashen Mali da Najeriya da ke makwabtaka da kasar in da 'yan ta'adda kamar Boko Haram suka yi kaurin suna.