1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin ta'addanci ya halla soja biyu a Nijar

Abdoulaye Mamane Amadou
October 8, 2019

A Jamhuriyar Nijar wasu sojoji biyu sun hallaka a yayin da wasu biyar suka jikkata a sakamakon wani batakashi da 'yan ta'adda a garin Dogon Kiria na jihar Dogondoutchi da ke Kudu maso yammacin kasar.

https://p.dw.com/p/3Qs6P
Mauretanien G5 Sahel Taskforce
Hoto: Getty Images/AFP/T. Samson

Ma'aikatar cikin gidan Nijar ta tabbatar da mutuwar jama'ian tsaron kasar biyo bayan wani dauki ba dadi da suka yi tare da galaba kan maharan masu dauke da muggan makaman yaki.

Wannan shi ne karo na biyu da wasu da ake kyautata zaton mayakan jihadi ne ke kai farmaki a jihar ta Dogondoutchi mai makwaftaka da Najeriya inda a baya maharan suka kai hari a kauyen Bagaji, da yayi sanadiyar hallaka jamai'an gendarme biyu da wani farar hula daya a cikin watan Afrilun wannan shekrara.