Nijar: Boko Haram ta halaka sojoji da dama | Labarai | DW | 30.10.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Nijar: Boko Haram ta halaka sojoji da dama

Akalla sojojin gwamnatin Nijar 12 sun halaka wasu da dama suka jikkata a cikin wani hari da ake zargin mayakan Boko Haram ne suka kai shi a kauyen Blabrine na Jihar Diffa kusa da iyaka da Tarayyar Najeriya.

Kamfanin dillancin labaran Jamus na DPA ya ruwaito gwamnan Jihar ta Diffa Malam Issa Lamine  kasar ta Nijar na cewa maharan sun kai farmakin ne tun da sanhin safiyar wannan Laraba a kauyen na Blabrime  kilomita 45 daga gabashin birnin N'Guigmi inda suka yi nasarar karbe kayayyakin yaki dama.

Sai dai ya kara da cewa sojojin gwamnatin sun shiga farautar maharan daga baya har a cikin Tabkin Chadi  inda suka yi nasarar kashe mayakan na boko Haram da dama kana suka karbo kotocin yaki biyu da tarin makamai.