Nigeria:Fina-finan Hausa na kaucewa a'aldu
April 10, 2018Talla
Tsoffin masu wasan kwaikwayo na arewacin Najeriya na nuna damuwarsu kan yadda matasan da ke wasan Hausa a yanzu, ke kwadayin tara dukiya a maimakon sanya aniyar kyautata tarbiyya tare da hadin kan al'umar Najeriyar. An dai jima da kokawa kan musamman yadda wasu fina-finan yanzun, ke kaucewa tsarin rayuwar al'ummar kasar, suna shiga na wasu nahiyoyin. Sai dai watakila ana ganin game da irin yadda jama'a ke ci gaba da yin tsokaci za a iya samun sauyi.