1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nigeria: Kokarin magance rikicin Niger Delta

Salissou BoukariAugust 5, 2016

Jami'an tsaro sun kama wasu mutane guda tara da ake zargi da bai wa 'yan tawaye wasu sinadarai da ake hada bama-bamai da su a yankin Niger Delta.

https://p.dw.com/p/1JcEy
Nigeria Abuja Babagana Monguno und Abayomi Gabriel Olonisakin
Janar Monguno tare da Abayomi Gabriel OlonisakinHoto: picture-alliance/dpa/N. Bothma

Da yake magana tare da wakillan wani kanfani na yankin Niger Delta kan wannan batu, Janar Mohammed Monguno da ke a matsayin mai bada shawara kan harkokin tsaro a Tarayyar ta Najeriya, ya ce wani bincike mai zurfi da aka aiwatar, ya nunar cewa an sace akalla kg 9000 na sinadaran hada ababe masu fashewa da kuma wasu ababen masu fashewa 16.450 inda aka sayar da su ta hanyar da ba ta gaskiya ba.

Janar din ya ce daga cikin wadanda aka kama akwai mai kula da runfar ajiye kayayakin na wani kanfani, da wani mai taimaka masa sannan da jami'an tsaro guda biyar. Kuma binciken ya nunar cewa, ababen da ake amfani da su wajen kai hare-haren, ana hadasu ne ta hanyar sinadirai na Nitrate da ake amfani da su wajen yin takin zamani.