NEMA na bada agaji bayan tashin bama-bamai a Jos | Siyasa | DW | 06.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

NEMA na bada agaji bayan tashin bama-bamai a Jos

Mutane 44 sun mutu kana wasu 47 suka samu raunuka sanadiyyar tashin tagwayen bama-bamai a garin Jos na Najeriya. Amma kuma Hukumar bada agajin gaggauwa ta na kula da wadanda hare-haren suka ritsa da su.

Hukumar bada agajin gaggawa ta NEMA ta ce tun bayan tashin bama-baman biyu, ta dukufa aikin bada taimako wajen diban wadanda suka rasa rayuaknsu zuwa asibitoci daban daban. Tuni ma ta samar da kayyayakin taimakon gaggawa ga asibitoci don bada kulawa ga marasa lafiya da ke kwance.

Jama'a na kan garzayawa asibitoci don duba 'yan uwa da dangoginsu da suka samu raunuka. Su kuwa kunguyoyi da ke aikin agajin gaggawa irin su Fitiyanus Islam, 'yan Agajin kungiyar Izala, dama 'yan kungiyar agaji ta Red Cross, sun dukufa aikin taimakawa jama'a wajen kai marasa lafiya asibitoci da kuma bada taimako na gaggawa.

Nigeria Potiskum Selbstmordanschlag 12.01.2015

'Yan uwan wadanda suka jikata ma na bada agaji

Rundunar 'yan sandan jihar Filato ta ce ta na kan tattara alkaluma na adadin mutanen da suka rasu, da masu raunuka. Gwamnan jihar Filato Simon Lalong, ya fitar da wata sanarwa inda ya yi Allah wadai da hare haren, kana ya yi kiran samun hadin kai tsakanin al'ummar jihar don yaki da masu tada irin wadannan bama-baman.

Sauti da bidiyo akan labarin