NATO zata tura dakaru dubu daya zuwa Pakistan | Labarai | DW | 22.10.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

NATO zata tura dakaru dubu daya zuwa Pakistan

Kungiyar tsaron arewacin tekun Atlantika wato NATO ta yi watsi da wata bukatar gaggawa da MDD ta yi na fara kai dauki ta sama ga wadanda suka tsira daga bala´in girgizar kasar da ta auku a arewacin Pakistan. Yanzu haka dai akwai dubun dubatan mutane makale a yankunan tsaunuka na arewacin Pakistan din. A maimakon haka kungiyar ta NATO ta ce zata tura dakarun kimanin dubu 1 da wasu juragen sama masu saukar ungulu da ba su taka kara su karya ba zuwa yankin. Yau makonni biyu bayan aukuwar girgizar kasar, har yanzu ba´a kai ga wasu dubban mutane da suka tsallake rijiya da baya sakamakon wannan bala´i daga Indallahi ba. Jami´an ba da agaji na fargabar cewa mutane da dama ka iya mutuwa saboda rashin kayan sanyi musamman a daidai wannan lokaci da sanyin hunturu ke karatowa a yankin na Himalaya.