1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

NATO da agajin sufuri a lardin darfur

zainab A MohammadJune 10, 2005

kungiyar tsaro ta NATO ta amince da agawa wajen jigilar dakarun Afrika

https://p.dw.com/p/BvbO
Hoto: AP

A jiya ne ministocin tsaro na kungiyar NATO suka amince da daukan nauyin jigilar dakarun Afrika zuwa lardin Darfur dake yammacin Sudan,wanda ke kasancewa na farkonsa a nahiyar Afrika.

Ministoci tsaro na kungiya NATo dai sun dauki lokaci mai tsawo suna mahawara na jaddada cewa babu gasa tsakanin kungiyar da ayyukan kungiyar gammayyar turai ,bayan faransa ta sanar dacewa gudummowa data bayar na daukan dakarun Senegal zuwa Sudan ,tayi shi ne akarkashin inuwan kungiyar EU amma ba Nato ba.

Wannan amana da kungiyar tsaro ta NATO tayi game da tallafin dai yazo yini guda ne gabannin bude taron tattauna warware rikicin Darfur din a birnin Abujan tarayyar Nigeria.

Dubban mutane nedai suka rasa rayukansu a rikicin na lardin Darfur,ayayinda wasu kimanin million 2 suka kaurace daga matsugunnensu,a wannan rikici da yanzu haka ya shiga shekara na uku.

Sakatare general na kungiyar tsaro ta NATO Jaap de Hoop Scheffer ya bayyana cewa halin da jamaa ke ciki a lardin Darfur na mai zama abun takaici ,wanda ya zamo wajibi wasu kungiyoyi da suka hadar da Eu su taimakawa kungiyar gamayyar Afrika ,wajen shawo kansa.

Kama daga ranar 1 ga watan Yuli nedai,kungiyar ta NATO zata bada jiragen da zasu fara jigilar dakaru daga Afrika zuwa Darfur.kungiyar gamayyar Afrika dai tuni tayi watsi da yiwuwan samun agajin dakarun kasashen yammaci a darfur,amma a watan Aprilu tayi kira ga kungiyar gamayyar turai dana tsaro ta NATO kan su bada gaji na sufuri.

Ayayinda Sudan a nata bangare tayi maraba da tallafi na Sufuri daga kumgiyar tsaro ta NATO,amma taki amincewa dakarunta su taka kasar.

Kungiyar gammayyar Afrika dai na shirin kara dakarun tsaron ta a lardin na Darfur zuwa 7,700 kama daga karshen watan Satumba.

A karkashin wannan shiri dai Rwanda tayi alkawarin bada Karin rundunoni 3,kana Senegal biyu da Nigeria biyu,ayayinda Afrika ta kudu zata bada Karin runduna guda,na dakarunsu domin tabbatar da tsaro a yammacin Sudan din.

Amurka dai ita zata dauki nauyin jigilar dakaru Rwanda,ayayinda Faransa zatayi jigilan na Senegal.Shi kuwa ministan tsaro na Ukrain Anatoly Hrytsenko yace kasarsa na laakari da bada gudummowarta a karkashin tallafin sufuri na kungiyar tsaro ta nato,kana Canadas itama tana shirin shiga wannan agaji.

Da farko dai Amurka ta bukaci NATO data dauki nauyin sufuri da horar da jamiai,amma faransa ta hakikance cewa yin hakan na nufin shiga harkokin tallafi ta kungiyar gamayyar turai ta dauki alhaki.

Shi kuwa ministan Tsaro na Jamus Peter Struck cewa yayi,Jamus zata bada gudummowa wajen jigilar dakarun zuwa Darfur,amma baya da wani tasiri ko a karkashin Nat one ko kuma a karkashin EU.Ayayinda Britania tace zatayi amfani da kungiyoyin biyu wajen bada gudummowanta wa Darfur,inji ministan tsaro John Reid.

Majiyar kungiyar tsaro ta NATo dai na nuni dacewa kasashen Netherland da Denmark sun bayyana manufarsu na agazawa wannan yunkuri

Wannan furuci na Faransa dai ya sake ruruta mahawara kan sabanin raayi dake tsakanin kungiyoyin biyu,adadi lokacin da kungiyar gamayyar turai ke kokarin nemarwa kanta suna na kasacewa zakara wajen samar da tsaro a duniya.