NATO ba za ta shiga yaki a Ukraine ba | Siyasa | DW | 05.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

NATO ba za ta shiga yaki a Ukraine ba

Shugabannin kungiyar NATO a taron koli da suka yi a Wales, sun tabbatar da goyon bayan su ga kasar Ukraine a ci gaba da rashin fahimtar juna tsakaninta da Rasha.

Shugaban Ukraine, Petro Poroschenko, ya baiyana fatan samun ci gaba a shawarwarin neman tsagaita bude wuta a yakin dake gudana a gabashin Ukraine. Poroschenko ya ce ya umurci mashawartansa su yiwa Rasha tayin tsagaita bude wuta idan har kasar ta amince da tsarin da ya gabatar na zaman lafiya a wannan yanki.

Janar sakatare na kungiyar NATO, Anders Fogh Rasmussen ya fadi a zauren taron na Newport a Wales cewar an sha jin jawabai daga Rasha a game da batun tsagaita bude wuta ko neman zaman lafiya, amma abin dake da muhimmanci shi ne abin da ke gudana a can gabashin Ukraine. Kungiyar NATO tana zargin Rashan ne da laifin tura dubban sojojinta zuwa Ukraine inda suke taimakawa 'yan kishin kasa masu neman ballewa, dake samun goyon bayan Rashan. Dangane da haka ne Rasmussen ya yi kira ga Rasha da cewar:

"Muna kira ga Rasha ta janye daga neman fada, ta kuma nemi hanyar zaman lafiya da kwanciyar hankali".

Taron kolin na shugabannin NATO a Newport ya zama na goyo baya ga manufofin shugaban Ukraine, Petro Poroschenko, akalla da fatar baka. Kungiyar ta ce ba zata yarda da shiga wani hali na yaki tsakaninta da Rasha ba, inji janar sakatare Ander Fogh Rasmussen. Sai dai ita ma shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel bata baiyana karfin zuciya a game da batun shawo kan rikicin na gabashin Ukraine ba, duk da ganawar da tayi da Poroschnko da sauran mahalarta taron na Newport. Duk da hakan, akalla an sami tuntubar juna tsakanin Poroschenko da shugaban Rasha, Vladimir Putin.

""To amma ko abubuwana da suka tatauna kansu za'a aiwatar da su a zahiri yau ko gobe ko nan da kwanaki masu zuwa, wannan abune da za'a jira tukuna a gani. Na lura da bukatar shugaban na Ukraine na samun sulhun siyasa kan lamarin. Na sha nunar da cewar ba zamu kai matsayin da zamu yi amfani da karfin soja domin neman sulhun wannan rikici ba.Wannan ra'ayi kuwa a yau ya sami goyon baya daga dukkanin wadanda suka shiga tattaunawar da muka yi, wato wakilan kungiyar NATO".

Sakamakon halin da ake ciki na a rashin tsaron da ya kamata a gabashin Turai, saboda rikicin Ukraine da Rasha, kungiyar NATO ta maida burinta na kare dukanin wakilanta. Janar sakatare Rasmussen ya ce dukkanmu muna da alkawari mai karfi na kare kanmu daga duk wani hari idan ya taso.

Mawallafi: Umaru Aliyu
Edita: Yusuf Bala

Sauti da bidiyo akan labarin