NATO: An yabawa matakin sulhunta rikicin Afghanistan | Labarai | DW | 03.09.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

NATO: An yabawa matakin sulhunta rikicin Afghanistan

Sakataren kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg ya bayyana cewar kungiyar za ta cigaba da bayar da goyon bayanta a kawo karshen rikici tsakanin 'yan Taliban da gwamnatin Afghanistan.

Tuni shugaba Donald Trump na Amirka ya sanar da shirin janye sojoji da yawansu ya kai dubu 8,600 daga kasar idan aka cimma daidaito a sulhun, an dai kwashe fiye da shekara guda tsakanin Amirka da Taliban ana laluben hanyoyin magance rashin jituwar da ke haifar da asarar rayuka da dukiyoyin gwamnati a Afghanistan.


Sakataren kungiyar tsaron ta NATO Jens Stoltenberg ya gana da shugabar hukumar zartarwar kungiyar tarayyar Turai Ursula von der Leyen a birnin Brussels game da batutuwan da suka shafi alakar kasashen ketare.