Narendra Modi ya kai ziyara Pakistan | Labarai | DW | 25.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Narendra Modi ya kai ziyara Pakistan

Firaministan Indiya Narendra Modi ya kai ziyarar bazata Pakistan don ganawa da takwaransa Nawaz Sharif kan batutuwa da dama ciki kuwa har da maganar yankin Kashmir.

Wannan dai ita ce ziyara irinta ta farko da wani shugaba daga Indiya kai cikin shekaru fiye da goman da suka gabata, sai da yayin taron sauyin yanayi da aka kammala a birnin Paris Frimanista Modi da Sharif sun yi wata takaitacciyar tattaunawa.

Da dama dai na kallon wannan ziyara a matsayin wata hanya da makotan biyu za yu yi amfani da ita wajen warware rigingimun da ke tsakaninsu wadanda suka tsanananta a 'yan shekarun da suka gabata.