Nan gaba a yau za a buda taron ƙoli na Majlisar Ɗinkin Dunia | Labarai | DW | 25.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Nan gaba a yau za a buda taron ƙoli na Majlisar Ɗinkin Dunia

Nan gaba a yau ne a birnin New York, na ƙasar Amurika, shugabanin ƙasashe da na gwamnatocin dunia, za su buɗa taron shekara –shekara, na Majalisar Ɗinkin Dunia.

A jilimilce, shugabanin 193 za su gabatar da jawabai.

A yau za a fara da sauraran Luis Ignacio Lula Da Sylva, na Brazil, Georges na Amurika , Mahamud Ahmadinedjad na Iran ,da kuma Nikolas Sarkozy na ƙasar France, wanda shine karo na farko, da ya harlarci wannan taro.

Kazalika, a yau ɗin shugaba Sarkozy, zai jagoranci taron komitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Dunia, a game da bututwan da su ka shafi kwanciyar hankali da tsaro a nahiyar Afrika.

A na sa ran a cikin wannan mahaura komitin sulhun ya rattaba akan wata bukata da France da gabatar masa ta aika rundunar kwantar da tarzoma a iyakokin Tchad da Jamhuriya Afrika ta tsakiya, domin tabbatar da tsaro a sakamakon ɓullar rikicin yankin Darfur a wannan yankuna.