Najeriya:′Yan sanda na fafutukar farautar masu satar mutane | Siyasa | DW | 04.04.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Najeriya:'Yan sanda na fafutukar farautar masu satar mutane

Wannan al'amari dai da farko an dan samu saukinsa amma kuma daga baya-baya nan lamarin ya kara lallacewa. A kasa da mako daya kawai goman mutane ne aka sace tsakanin hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Wannan al'amari dai da farko an dan samu saukinsa amma kuma daga baya-baya nan lamarin ya kara lallacewa. A kasa da mako dai kawai sama da mutane guda 30 aka sace tsakanin hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Hanyar jirgin kasa ta fi tabbas fiye da ta mota saboda masu yin sata da yin garkuwa jama'a

Darurruwan jama'ar ne a Jihar Kauna ta Najeriya ke yin tururruwar zuwa daukar jirgin kasa daga Kaduna zuwa Abuja domin kaucewa masu yin fashi a kan hanyoyin mota. Wadanda ke satar mutane tare da yin garkuwa da su domin neman kudaden fansa. Duk da irin kokarin da 'yan sanda suke yi na ciwo kan al'amarin har yanzu da sauran rina a kaba.

 

Sauti da bidiyo akan labarin