Najeriya:Fursunoni sun yi yunkurin tserewa | Labarai | DW | 28.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya:Fursunoni sun yi yunkurin tserewa

Fursunoni hudu sun rasa ransu bayan da 'yan sanda suka bindigesu, a lokacin da suka afkawa ma'aikatan dafa abinci a gidan yarin bayan da suka fasa kofar kurkukun da gatari.

Hukumar 'yan sandan jihar Akwa Ibom ta ce a yanzu sun cafke mutane bakwai da suka yi yunkurin tserewa daga gidan yari, amma ana ci gaba da farautar wasu fursunonin 36 da suka gudu.

Babu cikakkun bayanai kan adadin fursunoni da ke gidan yarin amma kungiyoyin kare hakkin bani Adam sun sha sukar hukumomin Najeriya kan rashin inganta rayuwar mutanen da ke kurkuku a fadin kasar.

Abinda wasu ke ganin baya rasa nasaba da abinda ke fusata fursunonin haddasa rigima da jami'an da ke tsaron kurkukun domin neman fita.