Najeriya: Zawarawa sun kai kamfanin Shell kara | Labarai | DW | 29.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya: Zawarawa sun kai kamfanin Shell kara

Cikin wadanda suka gabatar da karar dai akwai Esther Kiobel matar Barinem Kiobel, wanda aka ratayesu tare da marubucin nan dan fafutika Ken Saro-Wiwa a shekarar 1995.

Wasu mata hudu daga Kudancin Najeriya sun garzaya kotu a Holland don kalubalantar kamfanin Shell bisa zargin hannunsa a kisan da aka yi wa mazajensu a shekarun 1990, lokacin mulkin soja kamar yadda kungiyar kare hakkin bil Adam ta Amnesty International ta bayyana a wannan rana ta Alhamis.

Cikin wadanda suka gabatar da karar dai akwai Esther Kiobel matar Barinem Kiobel, wanda aka ratayesu tare da marubucin nan dan fafutika Ken Saro-Wiwa a shekarar 1995.

Wadannan mata dai da suka garzaya kotu da ke a birnin The Hague na neman abi hakkinsu kasancewar kamfanin na Shell na da hannu a wajen kame mazajensu, kafin daga bisani a kai ga kashesu a hannun gwamnatin soja, kisan da ya jawo tofin alatsine a duniya.