Najeriya: Zanga-zangar juyin juya hali | Labarai | DW | 05.08.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya: Zanga-zangar juyin juya hali

Jami'an tsaro sun yi amfani da barkonon tsohuwa wajen tarwatsa masu zanga-zangar neman sauyi a birnin Legas da ke kudancin kasar a wannan Litinin

Wani daga cikin masu gangamin, ya shedawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa, akwai wasu mutum biyu da suka ji rauni a sanadiyar harbin bindiga a yayin hargitsin sannan jami'an tsaro sun kama wasunsu.

Har wa yau, masu zanga-zangar sun nemi gwamnatin Najeriyar, da ta gaggauta sakin Sowore da aka cafke a karshen mako bayan da ya yi shelar jama'a su fito don yin juyin-juya hali a kasar daga wannan Litinin da zummar jan hankalin gwamnati don gyara lamuran kasar da suka tabarbare.

Masu gangamin na daga cikin rukunin da suka amsa kiran Omoyele Sowore, tsohon dan takarar kujerar shugabancin kasar a babban zaben 2019 da ya gabata a karkashin jami'yyar AAC mai adawa.