Najeriya za ta kashe Naira Tiriliyan shida a 2016 | Siyasa | DW | 08.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Najeriya za ta kashe Naira Tiriliyan shida a 2016

Faduwar farashin man fetir dai ya yi babban tasiri ga harkokin kashe kudade a gwamnatin ta Najeriya.

Gwamanatin Najeriya za ta kashe Naira tiriliyan shida a kasafin kudi na shekarar 2016 kamar yadda ministan kasafi da tsare-tsare a gwamnatin ta tarayyar Najeriya Udoma Udo Udoma ya bayyana a ranar Litinin.

Da ya ke jawabi ga manema labarai jim kadan bayan kammala zaman majalisar zartarwa a tarayyar ta Najeriya a Abuja fadar gwamnatin kasar, ministan ya ce kasafin na bana zai haure na shekarar 2015 da tiriyan daya.

A cewarsa kashi talatin cikin dari na wadannan kudade za a yi amfani da su ne wajen abubuwa da suka shafi raya kasa sabanin kashi 15 cikin dari da aka warewa wannan fanni a wannan shekara ta 2015.

Faduwar farashin man fetir dai ya yi babban tasiri ga harkokin kashe kudade a gwamnatin ta Najeriya inda ya shafi ayyukan da gwamnatin ke gudanarwa kai harma da batun biyan kudaden albashi a jihohin kasar, yayin da a bangare guda shugaba Muhammad Buhari ke bayyana cewa gwamnatin da ta gabata ta bar baitil malin gwamnati kusan ba komai.