1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasafin Naira triliyan 16 don manyan aiyuka a 2022

October 6, 2021

Sabon kasafin na Naira triliyan 16 da miliyan dubu dari uku na zaman mafi girma a cikin shekaru kusan bakwai na gwamnatin da APC ke jagoranta a Najeriya.

https://p.dw.com/p/41MAF
Nigeria Politik l Senat
Hoto: Getty Images/AFP/K. Sulaimon

Kuma babban burinsa na zaman dorawa da kila ma kammala daukacin manyan aiyukan kasar da Abujar ta faro.

Wajen wani taro a Abuja dai majalisar zartarwa ta kasar ta ce, ta amince bisa kasafin da ya kunshi kudin shigar da ya kai triliyan 10,  da kuma gibin da ya kai triliyan sama da shida.

Manya na aiyukan raya kasar dai za su lamushe triliyan shida a yayin da Abujar ta tsara cin bashin da ya kai na triliyan sama da biyar a shekarar badin.

A badin dai gwamnatin kasar ta dora kasafin kan dalar Amurka 57 kan kowace gangar mai da kuma iya hako ganga miliyan 1.8 a kusan kullum.

Shugaba Muhammadu Buhari
Shugaba Muhammadu BuhariHoto: Siphiwe Sibeko/REUTERS

Ana dai kallon kasafin da idanu na gada a tsakanin APC da ke fatan dorawa bisa mulki na kasar da kuma cika alkawuran da ke tsakaninta da al'ummar mai zabe.

Kuma daga dukkan alamu tasirin kasafin na shirin wuce batu na siyasar ya zuwa kokari na sauya makomar kasar da ke neman hanyoyi na ci gaba cikin tsananin rikicin rashin kudi.

A gobe Alhamis ne dai shugaban kasar zai gabatar da kasafin a gaban wani zaman majalisun tarayyar Najeriya na hadin gwiwa a Abuja.

To sai dai kuma abun da ke daukar hankali ya zuwa yanzu na zaman banbancin da ke tsakanin farashin danyen mai da gwamnatin kasar ta dora sabon kasafin kai da kuma farashin man da kasar ke samu yanzu.

A yayin da alal misali Abujar tai kasafin bisa dalar Amurka 57 kan ko-wace ganga, farashin danyen man ya haura dala 80 ya zuwa ranar yau.

Majalisar wakilai Abuja
Majalisar wakilai AbujaHoto: cc-by-sa/Shiraz Chakera

Tuni dai dama muhawara ta yi nisa cikin kasar bisa tasirin sabon kasafin ga 'yan kasar da ke shiri na adabo da gwamnatin 'yar sauyi  zuwa badi.

Auwal Mu'azu dai na sharhi bisa harkoki na tattali na arziki da zamantakewar al'umma ta kasar. Kuma a fadarsa  da kamar wuya kasafin yayi tasiri a cikin tsarin yakin neman zaben da ke neman mamaye harkokin Najeriyar a badi.

A badin dai kuma a fadar 'yan mulki tarrayar Najeriyar tana shirin kisan triliyan uku da miliyan dubu 600 domin biyan kudin ruwa na basukan da ke ta karuwa, kuma ke iya illa ga kokarin kasar na ci gaba.