Najeriya za ta daina shigo da kayan abinci daga waje | Labarai | DW | 14.08.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya za ta daina shigo da kayan abinci daga waje

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayar da umurni ga babban bankin kasar da ya daina ba da kudi domin shigo da kayan abinci a cikin kasar daga kasashen ketare.

Wannan mataki dai na cikin jajircewar da Najeriya ta dade tana yi na dogaro da kai a fannin kayan abincin wanda aka zaburar da harkar noma a ‘yan shekarun nan. Tun daga 2015 babban bankin kasar ya haramta samar da kudaden kasashen waje don shigo da kayayyaki har 41 wadanda ya tabbatar za’a iya samar da su a cikin kasar. A yanzu Shugaban Kasar Muhammadu Buhari ya yi mai gaba daya inda ya bai wa bankin umurnin haramta ba da kudadden kasashen waje don shigo da kayan abinci a kasar. Tuni manoma suka fara murna  da wannan mataki. Babban bankin Najeriya ya ce daga 2015  zuwa 2018 Najeriyar ta samu adana kudin kasashen waje har dalla bilyan 21 sakamakon haramta shigo da kayan abinci a kasar.

Sauti da bidiyo akan labarin