Najeriya za ta bincike zargi take hakkin dan Adam | Labarai | DW | 05.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya za ta bincike zargi take hakkin dan Adam

Kungiyar kare hakkin bil Adama ta zargi Najeriya da aikata laifukan yaki a yankin arewa maso gabashin kasar

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta zargi dakarun Najeriya da ke yaki da 'yan ta'addan Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar, da aikata laifukan yaki, kamar yadda wasu shaidu da aka tattara na faifan-bidiyo suka nuna.

Tuni mahukuntan Najeriya suka bayyana kaddamar da bincike, kan lamarin. Kungiyar Boko Haram mai kaifin kishin Islama ta yi kaurin suna wajen aiwatar da ayyukan rashin imani kan mutane musamman a yankin arewa maso gabashin kasar ta Najeriya.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Usman Shehu Usman