'Yan siyasa na dagula tsaron Najeriya
May 15, 2019Babban hafsan sojojin Najeriya Laftanar Janar Tukur Buratai ya zargi 'yan siyasa da suka fadi zabe da hannu wajen karuwar hare-haren 'yan bindiga da sace mutane a yi garkuwa da su don neman kudin fansa wanda ake fama da shi a shiyoyin Arewa maso Yammaci da Arewa ta Tsakiyar Najeriya.
"Kalubalen tsaro da muke fuskanta yanzu haka, ina da yakini na cewa ba za a rasa alakanta shi da zaben da aka kammala ba da dadewa ba, wasu 'yan siyasa da suka fadi zabe na daukar nauyin aiyukan na bata gari muna da shedu masu karfi, sai dai muna taka-tsantsan don kauce wa kuskure."
Janar Buratai ya yi wannan zargi yayin da yake jawabi ga mambobin kwamitin kula da harkokin sojoji na majalisar wakilai ta Najeriya wadanda suka je Maiduguri fadar jihar Borno domin samun bayanai a kan yadda ake samun tabarbarewar tsaro a Najeriya.