1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya:IMN ta yi kashedi kan batun ta'addanci

Gazali Abdou Tasawa
July 28, 2019

A Najeriya kungiyar 'yan uwa Musulmi ta mabiya mazhabin Shi'a ta IMN ta yi tir da Allah wadai da matakin gwamnatin Najeriya na neman saka ta a jerin kungiyoyin 'yan ta'adda. 

https://p.dw.com/p/3Mrde
Nigeria Schiitische Muslime in Dakasoye
Hoto: A. Abubakar/AFP/Getty Images

A wani taron manema labarai da ya kira a wannan Lahadi a birnin Abuja Yahiya Dahiru daya daga cikin shugabannin kungiyar ta IMN ya bayyana matakin saka kungiyar tasu a cikin jerin kungiyoyin 'yan ta'adda da wani babban hadari ,tare da jaddada cewa ba za su dakatar da gudanar da zanga-zanga ba matsawar ba a sakon shugaban nasu Cheik Ibrahim Alzakzaky ba. 

A Jiya Asabar ne dai wata kotun Birnin Abuja ta fitar da wani kudiri da ke bai wa gwamnatin Najeriyar hurumin saka kungiyar ta 'yan Shi'an ta IMN a jerin kungiyoyin 'yan ta'adda kuma haramtattu. Ya zuwa yanzu dai Shugaban kasar ta Najeriya Muhammadou Buhari bai kai ga ayyana wannan doka ba.

Matakin haramta wannan kungiya ta 'yan Shi'a dai ya biyo bayan wasu jerin zanga-zanga ne da mabiyan kungiyar suka yi ta gudanarwa a Birnin Abuja domin neman a sako jagoransu Sheik Ibrahim al-Zakzaky da hukumomin Najeriyar ke tsare da shi, zanga-zangar da mutane shida suka mutu a cikinta da suka hada da wani babban jami'in 'yan sanda.